Bayan shafe kwanaki 62 a tsare, wata babbar kotun jihar Ribas karkashin jagorancin Hon. Mai shari’a Chinwendu Nworgu, a safiyar Talata, ya bayar da belin dan majalisar wakilai, Hon. Farah Dagogo.
Dagogo, wanda ya kasance dan takarar gwamna a jam’iyyar PDP, yana fuskantar shari’a bisa zarginsa da aikata manyan laifuka.
An kama dan majalisar ne a ranar 22 ga Afrilu, 2022 a wurin da ake gudanar da atisayen tantance masu neman takarar gwamna a jam’iyyar a Fatakwal, kasa da kwanaki hudu bayan Gwamna Nyesom Ezenwo Wike ya bayyana cewa ana neman sa ne bisa zarginsa da daukar wasu da ake zargin ‘yan kungiyar asiri ne don kawo cikas wajen tantance masu neman tsayawa takarar gwamna a jam’iyyar. sakatariyar jam’iyya.