Wata babbar kotun tarayya da ke zamanta a Legas a ranar Talata ta bayar da belin tsohon gwamnan babban bankin Najeriya, CBN, Godwin Emefiele.
Kotu ta bayar da belin Emefiele a kan kudi Naira miliyan 20 da kuma wanda zai tsaya masa a daidai wannan adadi.
Hakan ya biyo bayan tuhume-tuhume biyu na mallakar makami ba bisa ka’ida ba da hukumar tsaron farin kaya ta DSS ta yi masa.
Lauyan Emefiele, Joseph Daudu, bayan da wanda yake karewa ya ki amsa laifuffukan da ake tuhumarsa da su biyu, ya nemi a bayar da belinsa, yana mai cewa laifin da aka tuhumi Emefiele na da beli.
Hukumar DSS dai ta dauko Emefiele ne kimanin wata daya da ya gabata bayan da shugaba Bola Tinubu ya dakatar da shi.
An gabatar da shi kotu ne a wata farar motar kirar Toyota Hilux, dauke da lambar a rufe, da misalin karfe 9:23 na safe.
Da isowar kotun, Emefiele ya sauka daga motar inda wata mata ta taimaka masa a gaban mai shari’a Nicolas Oweibo.


 

 
 