Wata babbar kotun tarayya da ke zamanta a Abuja ta bayar da belin babban Akanta Janar na Tarayya, Ahmed Idris da sauran wadanda ake tuhumarsa bisa sharuddan da hukumar yaki da masu yi wa tattalin arzikin kasa zagon kasa ta bayar.
Da yake yanke hukuncin, mai shari’a Adeyemi Ajayi ya ba da umarnin cewa wadanda ake tuhumar ba za su bar birnin tarayya ba, kuma idan sun so sai su nemi izinin kotu ko kuma a soke belinsu.
Kotun ta kuma bayyana cewa wadanda ake tuhumar za su rattaba hannu kan yarjejeniyar cewa za su bi sharuddan belin da EFCC ta gindaya.
Mai shari’a Ajayi ya kuma ba da umarnin cewa wadanda ake tuhumar kada su samu kuma ba za su sayi fasfo na daban ba har sai an kammala shari’ar, bayan sun ajiye fasfo dinsu na asali ga hukumar.
Alkalin kotun ya bayar da hukuncin ne bisa hujjar cewa har yanzu ba a tabbatar da zargin da ake yi wa wadanda ake tuhumar ba.Kotun ta kuma bayyana cewa, bisa tsarin doka, wadanda ake tuhumar suna da damar bayar da belinsu, duk da zargin da ake yi musu, tun da mai gabatar da kara bai bayyana cewa wadanda ake tuhumar sun aikata ba daidai ba a lokacin da suke hannun EFCC. In ji The Cable.
An fara shari’a kai tsaye bayan yanke hukuncin neman beli.