Wata babbar kotun tarayya da ke Abuja, ta bai wa Hukumar Yaki da yi wa Tattalin Arziki Tu’annati EFCC, izinin cafke tsohon Gwamnan Jihar Kogi, Yahaya Bello, a shirye-shiryen gurfanar da shi a ranar Alhamis.
Mai shari’a Emeka Nwite ne ya bayar da sammacin da yammacin Laraba a gaban hukumar EFCC.
Wannan dai na zuwa ne bayan da wata babbar kotun jihar Kogi ta yanke hukuncin hana EFCC kama tsohon gwamnan ko tsare shi ko kuma gurfanar da shi gaban kuliya.