Kotu ta yankewa Sheikh Abduljabar Kabara, hukuncin kisa ta hanyar rataya, tare da kwace dukkanin litattafan da ya gabatarwa da kotu, da kwace masallatansa guda biyu.
Kotun ta kuma harmta saka hoto da karatunsa a kowace kafar sadarwa.
Kotun da ake cikin birnin a jihar Kano, ta kuma tabbatar da Abduljabbar ya yi batanci ga Ma’aiki, sannan kuma ya gaza gabatarwa kotu hujjojin da za su gamsar da ita ikirarinsa na cewa a cikin litattafai ya ga abubun da ya fada akan Ma’aiki S. A. W.