Wani jirgin saman kamfanin Dana Air ya yi hatsari a filin jirgin sama na Murtala Muhammed da ke Legas.
Rahotanni na cewa lamarin ya faru ne da safiyar Talata.
Ba a sami asarar rai ba, yayin da ba a samu cikakkun bayanai da ke tattare da lamarin ba a lokacin hada wannan labarin.