Gwamnan jihar Kano, Dr. Abdullahi Ganduje da Farfesa Babagana Zulum, gwamnan Borno sun samu lambar yabo ta digirin girmamawa a babban taro karo na 25 na jamiāar jihar Legas.
Sauran mutanen da suka sami lambar yabo ta digirin girmamawa sun hada da: Mista Goodie Ibru, wanda ya kafa Sheraton Lagos Hotel Plc; Mrs Abike Dabiri-Erewa, shugabar hukumar āyan Najeriya mazauna kasashen waje (NIDCOM).
Mataimakin Shugaban Jamiāar Farfesa Ibiyemi Olatunji-Bello ne ya bayyana hakan a wajen taron laccaĀ karo na 25 a ranar Alhamis a Legas.
Olatunji-Bello ya ce, zabin da suka zaba daga cikin sunayen da aka ba da shawara bayan bincike mai zurfi sun tabbatar da gaskiyarsu, sadaukarwa da gudummawar hidima ga kasa.
āGanduje, bisa laāakari da irin gudunmawar da ya bayar wajen ci gaban bilāadama ana ba shi digiri na Dakta.