Jami’an tsaro tare da haÉ—in gwiwar ‘yan Bijilanti, sun fatattaki tawagar ‘yan bindiga yayin da suka kai hari yankin Gusau a jihar Zamfara.
Wani mazaunin yankin Magami dake Gusau, ya bayyana yadda jami’an suka tilasta wa yan ta’addan guduwa daga kai hari.
Rahoto ya nuna cewa, ‘yan bindiga sun jima suna yunkurin kai hari Magami dake karamar hukumar Gusau, amma ba su yi nasara ba.
Jaridar Daily Trust ta rawaito cewa, ‘yan bindigar a kan dandazon Babura sun yi yunkurin shiga garin da yammacin Lahadin nan, amma jami’an tsaro suka fatattake su.