Jamiāan tsaro na Civil Defence, sun kama wani matashi dan shekara 25 da ake zargin mai garkuwa da mutane ne dan asalin karamar hukumar Shongom a jihar Gombe, bisa zarginsa da yunkurin yin garkuwa da wani mutum mai suna Usman Mohammed dan shekara 70 a garin Koburga da ke iyaka da Billiri, karamar Hukumar Kaltungo.
Rahotanni ya nuna cewa, Lawal ya yi wa wanda abin ya shafa raunuka daban-daban a sassan kunne da kafada.
Da yake gabatar da wanda ake zargin a ranar Talata, Kwamandan jihar Waziri Goni ya bayyana wanda ake zargin Lawal a matsayin mai garkuwa da mutane wanda ya baiwa jamiāan tsaro wahala a baya, inda ya kara da cewa, ya yi barna da āyan kungiyar sa.
Goni ya bayyana cewa, rundunar ta samu nasarar dakile harin ne ta hanyar hadin gwiwar mazauna yankin, inda ya bukace su da kada su yi kasa a gwiwa wajen samar da sahihin bayanai da za su sa jihar ta samu zaman lafiya.
A cewar Kwamandan, Lawal ya gudanar da aiki a kewayen Shongom, Billiri, da Kaltungo. Ya kama mutane ana neman kudin fansa da kisa.
āSauran āyan kungiyar, kusan hudu, sun gudu da bindigogin AK-47 da wasu bindigu. Su ne āyan banga da ke yawo a cikin babban birnin Gombe, sun ba jamiāan tsaro ciwon kai. Alhamdu lillahi muna da daya daga cikinsu da wasu kusan shida a gidan yari, sauran hudu kuma da yardar Allah za mu same su,ā inji shi.