Hukumar shirya jarabawar shiga jami’o’i ta kasa (JAMB), ta kayyade mafi karancin maki ga masu neman shiga jami’o’i a Najeriya 140.
Hukumar ta kuma tantance mafi karancin maki na Polytechnic a kan 100, yayin da na kwalejojin ilimi ta kayyade 100 ma.
An cimma matsayar ne a taron siyasa na shekarar 2023 kan shiga manyan makarantun Najeriya da ke gudana a cibiyar shari’a ta kasa da ke Abuja.


