Iyayen dalibai na kwashe ‘ya’yansu daga Kwalejin Gwamnatin Tarayya ta Kwali a Abuja, saboda fargabar hare-haren ‘yan bindiga.
Jaridar daily Truyst ta ruwaito cewa, tun da sanyin safiyar ranar Litinin iyayen daliban ke cincirindo zuwa harabar makarantar da ke kan babban titin Abuja zuwa Lokaja, domin kwashe ‘ya’yansu.
Iyayen yaran sun bayyana cewa, sun samu kiran waya ne daga hukumomin makarantar cewa, su zo su kwashe ‘ya’yansu, saboda fargabar da hukumomin makarantar ke ciki, kan wasu hare-hare da ‘yan bindiga suka kai wa wasu yankuna da ke makwabtaka da makarantar.