Ƙungiyar Islamic State (IS), ta yi iƙirarin kai wa ayarin motoci hari na shugaban Ƙaramar Hukumar Nganzai da ke Jihar Borno, inda ta ce, ta kashe ɗan sanda ɗaya.
Cikin wani iƙirari da ta wallafa a shafinta na dandalin Telegram, ƙungiyar ta ce, ta kai harin ne a kan titin zuwa Gajiram da Gajigana ta hanyar amfani da manyan makamai.
A cewar ƙungiyar, reshenta da ke ayyuka a yammacin Afirka mai suna West Africa Province branch (ISWAP) ne ya kai harin, inda suka kashe ɗan sandan tare da ƙona mota ɗaya a harin. A cewar BBC.
Sai dai ba ta faɗi sunansa shugaban ƙaramar hukumar ba, ammma rahotanni a Najeriya sun ce sunansa Honorabul Mamman Gadai kuma ba a ji masa rauni ba.