Shugaban Hukumar Zabe Mai Zaman Kanta ta Kasa (INEC), Farfesa Mahmood Yakubu, ya ce, za a ci gaba da yin rajistar masu kada kuri’a (CVR).
Farfesa Yakubu ya bayyana haka ne a wurin taron kidayar kuri’un matasa a Abuja a ranar Asabar, 25 ga watan Yuni.
An bada umarnin kawo karshen atisayen ne a ranar 30 ga watan Yuni, amma sakamakon yawan fitowar masu kada kuri’a da kuma kiran matasan Najeriya a shafukan sada zumunta, da kuma kungiyoyin farar hula, hukumar ta yanke shawarar tsawaita wa’adin rajista.
Ba a bayar da wani bayani kan sabon wa’adin ba, sai dai, an bayyana hakan ne a wani sako da aka wallafa a shafin Twitter na hukumar INEC a ranar Asabar.