fidelitybank

Da Dumi-Dumi: INEC ta cire sunan Alhassan Ado Doguwa daga wanda ya ci zabe

Date:

Hukumar zabe mai zaman kanta ta kasa (INEC) ta cire sunan shugaban majalisar wakilai Alhassan Ado Doguwa daga jerin sunayen wadanda suka lashe zaben.

Hukumar zabe ta bayyana shi a matsayin wanda ya lashe zaben da aka yi a mazabar Doguwa/Tudunwada da aka yi ranar 25 ga watan Fabrairu.

Jami’in da ya lashe zaben, Farfesa Ibrahim Adamu Yakasai a baya ya bayyana cewa Doguwa na jam’iyyar APC ya samu kuri’u 39,732 inda ya kayar da abokin hamayyarsa Yushau Salisu Abdullahi na jam’iyyar New Nigeria People’s Party (NNPP) wanda ya samu kuri’u 34,798.

Amma a cikin sabbin zababbun mambobin da aka fitar, sunan Doguwa bai fito fili ba.

Idan dai za a iya tunawa, biyo bayan rikicin zabe da aka samu a mazabar bayan kammala zaben, ā€˜yan sanda sun cafke Doguwa bisa zarginsa da hannu wajen kashe wasu mutane da kuma kona sakatariyar jam’iyyar NNPP, zargin da dan majalisar ya musanta da kakkausar murya.

Rundunar ā€˜yan sandan ta tabbatar da cewa akalla mutane uku ne suka mutu yayin da aka kona sakatariyar yakin neman zaben jam’iyyar NNPP da ke Tudunwada tare da kona mutane biyu har lahira.

Daga nan ne aka gurfanar da Doguwa a gaban kotun majistare kan zargin kisan kai, kone-kone da kuma mallakar makamai ba bisa ka’ida ba, daga bisani aka tsare shi a gidan yari.

Sai dai wata babbar kotun tarayya da ke Kano a ranar Litinin din da ta gabata ta amince da belin dan majalisar kan kudi naira miliyan 500, amma ta hana shi shiga mazabarsa a zaben gwamnoni da na ā€˜yan majalisar jiha da ke tafe.

www.punch news.ng

Subscribe to Our VIP Newsletter

[newsletter_signup_form id=1]

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here

Share post:

Popular

More like this
Related

Gwamnatin Tinubu ta kama-karya ce – Atiku

Tsohon mataimakin shugaban kasa, Atiku Abubakar ya ce, hare-haren...

An gayyaci El-Rufa’i ka n zargin tayar da rikici a Kaduna

Rundunar Ę“ansandan jihar Kaduna, sun buʙaci tsohon gwamnan jihar...

Badakalar Naira biliyan 1.17 ta sake kunno kai a gwamnatin Kano

Rikicin rashawa da ya dabaibaye gwamnatin jihar Kano ya...

Ba za mu daga kafa ga duk wanda ya takale mu ba – China

Shugaba Xi Jinping na China, ya ce babu wani...

Nigeria Air ba na bogi ba ne – Hadi Sirika

Tsohon Ministan sufurin jiragen sama na Najeriya, Hadi Sirika,...

Amurka ta mika wa Najeriya tallafin abinci miliyan 32.5

Gwamnatin Amurka ta bayar da tallafin dala miliyan 32.5...

Gwamnatin Kano ta gargadi kungiyar ACF

Gwamnatin jihar Kano ta gargaɗi ʙungiyar Arewa Consultative Forum...

Operation Kukan Kura ya yi aiki sosai a Kano – CP Bakori

Hukumar ā€˜Yan Sanda ta Jihar Kano ta kaddamar da...

An sanya dokar ta bace a Makabartun Kano

Shugaban ʙaramar hukumar Nassarawa a Kano Honarabul. Yusuf Shuaibu...

An ga ‘Yar shekara 13 Fatima a rataye a Kano

Iyaye da sauran ā€˜yan uwa na cikin juyayi kan...

‘Yansanda sun kama Linga da Guchi rikakkun ‘yan Daba a Kano

Rundunar ’yan sandan jihar Kano ta kama Mohammed Isma’il...

Tinubu ya sauka da kwari bayan ya dawo daga Brazil

Shugaba Bola Ahmed Tinubu ya koma Najeriya bayan kammala...
X whatsapp