Sanata Kabiru Marafa na jihar Zamfara ya musanta rahotannin da ke cewa, shi da tsohon gwamnan jihar, Abdulaziz Yari sun fice daga jam’iyyar APC zuwa jam’iyyar PDP.
Marafa a yammacin Lahadin da ta gabata yayin wata hira da Tambarin Hausa, ya ce; “Abin da muka sani shi ne muna tattaunawa da jam’iyyun siyasa da dama da suka gayyace mu mu shiga cikin su a jihar.”
“A yanzu duk wani labarin da aka ce mun yi murabus, karya ne.”
“Abin da na sani shi ne, akwai jam’iyyun siyasa da dama, ba PDP kadai ba, wadanda suka gayyace mu suna son mu shiga har zuwa yanzu muna tattaunawa da su.”
“A iyakar sanina har ya zuwa yanzu ba mu cimma matsaya da kowa ba…Ba gaskiya ba ne cewa mun koma PDP, duk wanda ya fadi haka ya yi kuskure.”
“A matsayi na, ina kira ga mutane da su yi watsi da duk wani bayani game da batun daga kowane mutum, har sai sun ji ta bakinmu, … Har yanzu ba mu yanke shawara ba.”