Tsohon Ministan Sufurin Jiragen Sama, Hadi Sirika, ya isa babban birnin tarayya Abuja domin gurfanar da shi a gaban kuliya bisa zargin almubazzaranci da dukiyar al’umma.
A yau Alhamis ne ake sa ran hukumar yaki da masu yi wa tattalin arzikin kasa zagon kasa ta EFCC za ta gurfanar da Sirika a gaban kuliya bisa zarginsa da almundahanar Naira biliyan 2.7 a kan damfarar aikin jirgin Najeriyar.
Za a gurfanar da shi a gaban mai shari’a Sylvanus Oriji na babban kotun birnin tarayya Abuja.