Gwamnonin jam’iyyar PDP da aka fi sani da G5, sun yi tattaki zuwa kasar Spain domin gudanar da wani muhimmin taro a cikin rikicin da ya dabaibaye jam’iyyar.
Jaridar The Nation ta tattaro cewa gwamnonin sun bar kasar zuwa Madrid ne a daren Juma’a sa’o’i bayan da Gwamnan Ribas ya kara zarge-zarge a kan Shugaban Jam’iyyar Iyorchia Ayu.
Wadanda ke cikin jirgin Wike sune Gwamna Seyi Makinde (Oyo); Okezie Ikpeazu (Abia) da Samuel Ortom (Benue) a matsayin gwamnan jihar Enugu, Ifeanyi Ugwuanyi na iya shiga daga baya.
Ku tuna cewa Wike, yayin wata tattaunawa da manema labarai a Fatakwal a ranar Juma’a, ya kara zarge-zarge a kan Ayu yana mai cewa shugaban jam’iyyar na kasa ba shi da kima wajen jagorantar yakin neman zaben jam’iyyar a 2023.
Bayan kammala zaben fidda gwani na shugaban kasa na jam’iyyar, gwamnonin da suka fusata sun dage cewa rashin adalci ne jam’iyyar ta samu shugaban kasa da dan takarar shugaban kasa daga Arewa.
Sun ce har sai Ayu ya ajiye mukaminsa na shugaban jam’iyyar, za su yi watsi da dan takarar shugaban kasa na jam’iyyar, Atiku Abubakar a zaben 2023.