fidelitybank

Da Dumi-Dumi: Gwamnonin APC sun tattauna da Buhari a kan taron jam’iyyar

Date:

Gwamnonin jam’iyyar APC sun gana da shugaba Buhari a fadarsa da ke Abuja a ranar Laraba, ƙarƙashin jagorancin shugaban gwamnonin kuma gwamnan jihar Kebbi, Abubakar Atiku Bagudu.

Gwamnonin sun ce sun tattauna da Bahari kan batutuwa da dama musamman game da babban taron Jam’iyyar na ranar Asabar inda za a zaɓi shugabannin jam’iyyar.

Ganawar na zuwa a daidai lokacin da jam’iyyar APC mai mulkin Najeriya ke ci gaba da fuskantar baraka da rashin jituwa tsakanin jiga-jiganta kan babban taro na kasa da kuma zaben shugabanninta.

Tuni jam’iyyar ta kebe wa yankunan kasar mukamai daban-daban, inda misali aka kebe wa yankin Arewa ta tsakiya kujerar shugaban jam’iyya na kasa.

Shugaban Buhari na kokarin ganin an kauce wa kada kuri’a wajen zaben shugabanni, a maimakon haka yake neman a sasanta tsakanin ‘yan takara, yayin da gwamnonin jihohi ke cewa za su goyi bayan duk wanda shugaba Buhari ya ce a ba kujerar shugabancin jam’iyyar.

Sai dai wasu kusoshin jam’iyyar sun bayyana cewa ba su yarda da wannan tsari ba, kamar tsohon gwamnan jihar Zamfara Abdulaziz Yari, wanda ya ce, zai ci gaba da fafutikar neman kujerar shugaban jam’iyyar duk da cewa ba yankinsu ne aka kebe wa kujerar ba, kuma a ganinsa bai wa wani yanki ko wani mutum mukamin ba tare da zabe ba, rashin adalci ne.

mmm.nnn

Subscribe to Our VIP Newsletter

[newsletter_signup_form id=1]

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here

Share post:

Popular

More like this
Related

Gwamnatin Tinubu ta kama-karya ce – Atiku

Tsohon mataimakin shugaban kasa, Atiku Abubakar ya ce, hare-haren...

An gayyaci El-Rufa’i ka n zargin tayar da rikici a Kaduna

Rundunar ƴansandan jihar Kaduna, sun buƙaci tsohon gwamnan jihar...

Badakalar Naira biliyan 1.17 ta sake kunno kai a gwamnatin Kano

Rikicin rashawa da ya dabaibaye gwamnatin jihar Kano ya...

Ba za mu daga kafa ga duk wanda ya takale mu ba – China

Shugaba Xi Jinping na China, ya ce babu wani...

Nigeria Air ba na bogi ba ne – Hadi Sirika

Tsohon Ministan sufurin jiragen sama na Najeriya, Hadi Sirika,...

Amurka ta mika wa Najeriya tallafin abinci miliyan 32.5

Gwamnatin Amurka ta bayar da tallafin dala miliyan 32.5...

Gwamnatin Kano ta gargadi kungiyar ACF

Gwamnatin jihar Kano ta gargaɗi ƙungiyar Arewa Consultative Forum...

Operation Kukan Kura ya yi aiki sosai a Kano – CP Bakori

Hukumar ‘Yan Sanda ta Jihar Kano ta kaddamar da...

An sanya dokar ta bace a Makabartun Kano

Shugaban ƙaramar hukumar Nassarawa a Kano Honarabul. Yusuf Shuaibu...

An ga ‘Yar shekara 13 Fatima a rataye a Kano

Iyaye da sauran ‘yan uwa na cikin juyayi kan...

‘Yansanda sun kama Linga da Guchi rikakkun ‘yan Daba a Kano

Rundunar ’yan sandan jihar Kano ta kama Mohammed Isma’il...

Tinubu ya sauka da kwari bayan ya dawo daga Brazil

Shugaba Bola Ahmed Tinubu ya koma Najeriya bayan kammala...
X whatsapp