Hukumar kula da ilimin bai daya ta jihar Kaduna, KADSUBEB, ta ce, ta kori malamai 2,357 da suka fadi jarabawar cancanta da aka yi kwanan nan.
Mai magana da yawun ta, Misis Hauwa Mohammed, a cikin wata sanarwa ranar Lahadi a Kaduna, ta ce hukumar ta gudanar da jarabawar tantance malamai fiye da 30,000 a watan Disambar 2021.
Ta ce malaman makarantun firamare 2,192 da suka hada da shugaban kungiyar malamai ta kasa (NUT), Mista Audu Amba, an sallame su ne saboda sun ki zana jarabawar cancanta.
Ta ce an kuma kori wasu malamai 165 daga cikin 27,662 da suka zana jarabawar cancantar aiki saboda rashin nuna kwazo. In ji Vanguard.
Ku tuna cewa gwamnatin Kaduna a shekarar 2018 ta kori malamai 21,780 da suka fadi jarrabawar cancanta, sannan ta maye gurbinsu da wasu 25,000 da aka dauka ta hanyar kwazo.