fidelitybank

Da Dumi-Dumi: Gwamnati ta tsige mukaddashin Akanta na kasa

Date:

Gwamnatin tarayya ta cire mukaddashin babban akanta Mr. Chukwuyere N. Anamekwe, inda aka maye gurbinsa da Mr. Okolieaboh Ezeoke Sylvis, wanda tsohon darakta ne a tsarin asusun gwamnati na bai-daya, wato, TSA (Treasury Single Account).

Rahotanni na cewa, an maye gurbin mai rikon mukamin na Akanta-Janar din ne saboda hukumar yaki da masu yi wa tattalin arzikin kasar zagon-kasa, EFCC, na bincike a kansa.

A cewarrhotanni, gwamnatiun ba ta ji dadin wasu kalamai da ya yi ba inda ya ce, Najeriya na ranto kudi domin ta biya albashi.

Anamekwe wanda aka nada shi a wannan matsayi na rikon-kwarya a ranar 22 ga watan Mayu bayan da hukumar EFCC ta kama Babban Akantan kasar, Ahmed Idris bisa zargin almundahana da naira biliyan 80, ya yi kalaman cin bashin ne, a ranar 14 ga watan Yuni, na 2022, kuma kwana bakwai daga nan aka cire shi.

Mista. Sylva, wanda ke zaman mukaddashin Babban Akantan a yanzu, rahotanni na nuni da cewa zai yi ritaya a cikin watanni uku na farkon shekara mai zuwa, 2023.

Tuni dai gwamnatin tarayya ta kaddamar da neman wanda za ta nada a matsayin sabon Babban Akantan, kamar yadda bayanai ke nunawa.

Jaridar The Nation ta Najeriyar ta ruwaito cewa, duk wani kokari da ta yi na neman gaskiyar kalaman da Anamekwe ya yi cewa gwamnati na ciyo bashi ta biya albashi, ya ci tura.

thisday nigeria news

Subscribe to Our VIP Newsletter

[newsletter_signup_form id=1]

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here

Share post:

Popular

More like this
Related

Gwamnatin Tinubu ta kama-karya ce – Atiku

Tsohon mataimakin shugaban kasa, Atiku Abubakar ya ce, hare-haren...

An gayyaci El-Rufa’i ka n zargin tayar da rikici a Kaduna

Rundunar ƴansandan jihar Kaduna, sun buƙaci tsohon gwamnan jihar...

Badakalar Naira biliyan 1.17 ta sake kunno kai a gwamnatin Kano

Rikicin rashawa da ya dabaibaye gwamnatin jihar Kano ya...

Ba za mu daga kafa ga duk wanda ya takale mu ba – China

Shugaba Xi Jinping na China, ya ce babu wani...

Nigeria Air ba na bogi ba ne – Hadi Sirika

Tsohon Ministan sufurin jiragen sama na Najeriya, Hadi Sirika,...

Amurka ta mika wa Najeriya tallafin abinci miliyan 32.5

Gwamnatin Amurka ta bayar da tallafin dala miliyan 32.5...

Gwamnatin Kano ta gargadi kungiyar ACF

Gwamnatin jihar Kano ta gargaɗi ƙungiyar Arewa Consultative Forum...

Operation Kukan Kura ya yi aiki sosai a Kano – CP Bakori

Hukumar ‘Yan Sanda ta Jihar Kano ta kaddamar da...

An sanya dokar ta bace a Makabartun Kano

Shugaban ƙaramar hukumar Nassarawa a Kano Honarabul. Yusuf Shuaibu...

An ga ‘Yar shekara 13 Fatima a rataye a Kano

Iyaye da sauran ‘yan uwa na cikin juyayi kan...

‘Yansanda sun kama Linga da Guchi rikakkun ‘yan Daba a Kano

Rundunar ’yan sandan jihar Kano ta kama Mohammed Isma’il...

Tinubu ya sauka da kwari bayan ya dawo daga Brazil

Shugaba Bola Ahmed Tinubu ya koma Najeriya bayan kammala...
X whatsapp