Gwamnatin tarayya ta tabbatar da fara kwashe ‘yan Najeriya da suka makale a kasar Sudan, bayan barkewar rikici a kasar da ke arewacin Afirka.
Ministan Harkokin Waje, Geoffrey Onyeama da takwaransa, Karamin Minista Zubairu Dada, ne suka tabbatar da hakan a ranar Laraba yayin da suke yi wa manema labarai karin haske game da abubuwan da ke faruwa game da rikicin.
Onyeama ya bayyana cewa tuni motocin bas na alfarma guda 40 suka sauka a kasar Sudan domin daukar ‘yan Najeriya da ke kasar zuwa Masar inda za a dawo da su gida.
Ya ce ofishin jakadancin Najeriya da ke kasar Sudan da kuma hukumomin hukumar bayar da agajin gaggawa ta tarayya FERMA ne ke gudanar da aikin kwashe mutanen.
A cewar Ministocin, an dauki hayar motocin bas din da ke jigilar ‘yan kasar a kan kudi dala miliyan 1.2, inda suka ce sun hada da kudin samar da tsaro yayin jigilar su zuwa kasar Masar.
Ministocin biyu sun kuma yi nuni da cewa, za a bai wa mata da kananan yara fifiko, ciki har da jami’an diflomasiyya wadanda ke da hannu a cikin ayyukan kwashe mutanen.
Sun yi nuni da cewa gwamnatin Najeriya na yin amfani da yarjejeniyar tsagaita bude wuta na sa’o’i 72 don kwashe ‘yan Najeriya da dama.
Ambasada Dada ya bayyana cewa, tuni gwamnatin Saudiyya ta kwashe wasu ‘yan Najeriya ta cikin teku, domin tsira da rayukansu, kuma da zarar lamarin ya lafa za a yi shirin mayar da su Najeriya.