Gwamnatin jihar Zamfara ta nesanta kanta da nadain rawani da Sarkin Birnin Yandoto ya yi wa wani gungun ‘yan fashi da makami mai suna Ada Aleru da ke karamar hukumar Tsafe a jihar.
Dangane da haka gwamnan jihar Bello Mohammed Matawalle ya bayar da umarnin dakatar da Sarkin nan take.
Hakan na kunshe ne a cikin wata sanarwa da sakataren gwamnatin jihar (SSG) ya fitar kuma ya mika wa jaridar Nigerian Tribune.
Don haka gwamnan ya amince da nada kwamitin da zai binciki lamarin da ya kai ga matakin da sarkin ya dauka.
“Rukunin kwamitin shine kamar haka: Hon Yahaya Chado Gora, Shugaban; Hon. Yahaya Mohd Kanoma; mamba, Muhd Umar B/Magaji; Lawal Abubakar Zannah, Isa Muhd Moriki (Rtd P/Sec), Musa Garba, Sakatare.
Sanarwar ta ci gaba da cewa, “A halin da ake ciki, Alhaji Mahe Garba Marafa, wanda shi ne Hakimin Yandoto, an nada shi don jagorantar al’amuran masarautar.
Idan dai ba a manta ba a ranar Asabar da ta gabata ne sarki Garba Marafa, ya nada wa ‘yan fashin rawani a matsayin Sarkin Fulani a wani biki da ya samu halartar ‘yan bindiga akalla 100.