Wata gobara ta tashi a majalisar dokokin jihar Kogi, duk da ba a dai san musabbabin tashin gobarar ba har zuwa lokacin hada wannan rahoto da safiyar ranar Litinin.
DAILY POST ta tattaro cewa dakin taron ya kone gaba daya.
Gobarar ta tashi ne da misalin karfe 8 na safiyar ranar Litinin.
Kakakin majalisar, Prince Mathew Kolawole, a lokacin da yake zantawa da manema labarai a harabar majalisar ya ce, majalisar za ta baiwa hukumomin tsaro damar gudanar da bincike kan lamarin.
Sai dai ya ce, hakan ba zai hana majalisar gudanar da ayyukanta ba kamar yadda kudurin majalisar ya tsaya kan Dangote Cement Plc.