Wani sansanin ‘yan gudun hijira da ke kusa da yankin Muna a karamar hukumar Jere a jihar Borno dake Arewa maso Gabas ya kone kurmus.
A cewar Jaridar Leadership, kawo yanzu dai ba a bayyana cikakken bayanin faruwar lamarin ba, amma an sanar da hukumar bada agajin gaggawa ta kasa (NEMA), domin shawo kan lamarin.