Wasu da ba a san ko su waye ba sun kona ofishin hukumar zabe mai zaman kanta ta kasa (INEC), a karamar hukumar Igboeze ta Arewa a jihar Enugu.
Ofishin da ke shelkwata karamar hukumar da ke yankin Ogurute a jihar ya kone kurmus a daren Lahadi bayan da masu laifin suka mamaye yankin.
An tattaro cewa, hukumar kashe gobara ta jihar da ke da ofishi a Ogurute ta kasa shiga domin ceto lamarin, saboda fargabar sake kai hare-hare har sai an samar da tsaro.
Sai dai an gano cewa, a lokacin da aka samar da tsaro, gobarar ta kone ginin gaba daya. Kamar yadda jaridar The Nation ta ruwaito, motocin kashe gobara biyu daga Nsukka da Ogurute ne kawai suka iya yi shi ne hana gobarar bazuwa zuwa ofisoshin da ke kusa.
A halin da ake ciki, wani matashi wanda har yanzu ba a tantance ko wanene ba ya mutu a lokacin da yake kokarin dauke wasu igiyoyin wuta daga na’urar taranfoma a yankin Okija da ke jihar Anambra.