Firaministan Rwandan, ya sauka daga muƙaminsa tare da neman afuwar ‘yan ƙasar saboda shan barasa a lokacin da yake tuƙi.
Gamariel Mbonimana ya ajiye muƙaminsa kwana guda bayan da shugaban ƙasar Paul Kagame ya soke shi kan yin tuki a lokacin da ya sha barasa.
A wata sanarwa da ya wallafa a shafinsa na Twitter mista Mbonimana ya nemi afuwar ‘yan ƙasar da kuma shugaban ƙasar yana mai alƙawarta cewa ”ba zai sake shan giya ba”.
Tuƙi yayin da aka sha barasa laifi ne a ƙasar, da tararsa ta kai dala 140, tare da ɗaurin kwana biyar idan an kama shi.
Yayin da yake wani jawabi a ƙarshen mako shugaban ƙasar Paul Kagame ya soki ‘yan sandan ƙasar kan rashin kama firaministan, saboda ”kariyar” da yake da ita.
Mista Mbonimana shi ne firaministan ƙasar tun shekarar 2018, mamba ne a jam’iyyar Liberal Party wadda ke kawance da jam’iyyar RPF ta shugaba Kagame mai mulkin ƙasar.