Firaministan Italiya Mario Draghi ya yi murabus sakamakon rasa goyon bayan jam’iyyu uku da ya yi na gwamnatin haɗaka a ƙasar.
Tuni ya sanar da Shugaba Sergio Mattarella matakinsa na yin murabus.
Shugaban kasar ya nemi Mista Draghi ya ci gaba da riƙe muƙamin na Firaminista a matsayin rikon kwarya zuwa lokacin da za a gudanar da zabe, wanda ake sa ran yi zuwa watan Satumba.
Ana yaba wa Mario Draghi kan ci gaban da ya samar a fannin tattalin arzki a Italiya, kuma matakin murabus ɗinsa ya yi tasiri ga kasuwar hada-hadar hannayen jari.
Kuri’ar jin ra’ayoyin jama’a da aka gudanar ta nuna galibin Italiyawa na son Mista Draghi ya ci gaba riƙe mukaminsa. In ji BBC.