Tsohon gwamnan jihar Ekiti, Ayodele Fayose, ya fice daga jamâiyyar PDP, ya kuma bar siyasar bangaranci.
Wannan dai na zuwa ne kwana guda bayan da PDP ta sha kaye a zaben shugaban kasa da jam’iyyar All Progressives Congress, APC.
Fayose ya bayyana murabus din sa ne a lokacin da ya fito a matsayin bako a gidan talabijin na ARISE TV.
Ya kuma bayyana cewa dan takarar shugaban kasa na jam’iyyar PDP, Atiku Abubakar ya ki amincewa da tayin wa’adin mulki daya domin samun goyon bayan gwamnonin G5.
Atiku ya sha kaye a jihohin G5 a hannun dan takarar APC Bola Tinubu wanda ya lashe uku, kuma dan takarar jamâiyyar Labour Obi ya lashe jihohi biyu.
Da yake sanar da murabus dinsa, Fayose ya ce, “Daga yau, na daina PDP.”