Kamfanin Meta mai mallakin shafukan Facebook da Instagram da kuma WhatsApp, ya bayyana cewa zai rage kashi 13 cikin 100 na ma’aikatansa.
Abin da ke nufin kamfanin zai kori ma’aikata 11.000 daga cikin ma’aikatansa 87,000 a fadin duniya.
A wata sanarwa da shugaban kamfanin Mark Zuckerberg ya fitar, ya ce rage ma’aikatan na daga cikin wasu sauye-sauye masu tsanani da kamfanin ya gudanar a tarihinsa.
Shi ma dai kamfanin Twitter ya bayyana rage rabin ma’aikatansa a fadin duniya.
A wani labarin kuma kuma kamfanin na Twitter ya bayyana korar kusan duka ma’aikatansa a kasar Ghana.
Wata majiya ta shaida wa BBC cewa ma’aikaci daya ne kawai kamfanin bai kora ba, daga cikin ma’aikata kusan 20 da yake da su a kasar.