Jami’an hukumar Hukumar Yaki da yi wa Tattalin Arziki Tu’annati (EFCC) sun kama wasu mutane 92 da ake zargi da damfarar yanar gizo (wato Yahoo Boys) a wani samame da suka kai a wurare daban-daban a garin Fatakwal na jihar Ribas.
A wata sanarwa da hukumar ta EFCC ta fitar a ranar Juma’a ta hannun shugabanta, kafafen yada labarai da wayar da kan jama’a, Wilson Uwujaren, ya ce an kama wadanda ake zargin ne da laifin zamba ta yanar gizo a Choba da Ada George axis na Fatakwal, biyo bayan rahoton sirri.
Sanarwar ta ce binciken da aka yi na na’urorin da aka gano daga hannun wadanda ake zargin sun nuna cewa 64 daga cikinsu na da abubuwan da ba su dace ba a cikin wayoyinsu da sakwannin imel.