Hukumar Yaki da yi wa Tattalin Arzikin Kasa Ta’annati (EFCC), ta kama wasu mutane 18 da ake zargi da damfarar Intanet a Abuja.
A cewar wata sanarwa da hukumar ta fitar, an kama wadanda ake zargin ne a ranar 4 ga watan Yuli, 2022, a unguwar Trademore Estate, Lugbe, Abuja, biyo bayan samun rahotannin sirri kan zargin da ake yi musu na damfara a Intanet.
Wadanda ake zargin sune: ThankGod Oche, Joshua Olehja, Adamu Abdulkadir, David Bruno Bidemi, Emmanuel Avoh, Micheal Oche, Francis Abbah, Kayode Itodo, Shedrack Chibuike da Okeowo Elijah.
Sauran sun hada da: Victor Emmanuel, Emmanuel Edache, Abah Joseph Theophilus, Sunday Agidani, Elijah Adamu, Emmanuel Ahme, Moses Agada da Adacole Michel.
Kayayyakin da aka kwato daga hannun wadanda ake zargin sun hada da mota kirar Lexus, kwamfutocin tafi da gidanka, da wayoyin hannu.