Hukumar yaki da masu yi wa tattalin arzikin kasa zagon kasa, EFCC, ta cafke tsohon ministan sufurin jiragen sama, Hadi Sirika, bisa zargin tafka almundahana a kan aikin samar da jirgin Najeriyan Air.
Tsohan ministan, wanda ake ci gaba da bincike a kan sama da biliyan 8, ya isa ofishin hukumar yaki da cin hanci da rashawa EFCC babban birnin tarayya Abuja da misalin karfe 1:00 na rana a ranar Talata.
Majiyar EFCC da ta tabbatar da kamun, ta ce a halin yanzu ana cigaba da bincikarsa a ofishin EFCC da ke Wuse 2, Abuja.