Rahotanni sun bayyana cewa, hukumar tsaro ta farin kaya, DSS, ta kama Doyin Okupe, tsohon Darakta-Janar na kungiyar yakin neman zaben shugaban kasa, Peter Obi.
Rahotanni sun ce an kama Okupe ne ranar Alhamis a filin jirgin sama na Muritala Muhammed da ke Legas.
Daya daga cikin lauyoyinsa, Tolu Babaleye ne ya bayyana hakan a safiyar ranar Alhamis.
“Bayanin da ke zuwa gare ni yanzu shine, DSS sun kama Dr Doyin Okupe a filin jirgin sama na Legas akan hanyar sa ta zuwa Landan.
“Dalilin da ya sa a cewar majiyar shi ne, an nemi ya kawo hujjojin da ke nuna cewa babbar kotun tarayya da ke Abuja ta sake shi daga shari’ar da aka yanke masa tare da biyan tara tarar sanin duniya baki daya kuma aka ba shi izinin tafiya. gida,” in ji shi.