Wakilan jam’iyyar PDP a wajen cibiyar tattara sakamakon zaben shugaban kasa dake gudana a Abuja.
Wakilan karkashin jagorancin Sanata Dino Melaye, sun koka cewa, kamar ba za a yi musu adalci ba.
Sai dai shugaban hukumar zabe mai zaman kanta ta kasa INEC, Farfesa Mahmud Yakubu, ya bayyana cewa, a tsarin su dole ne su karanti sakamakon jihohin da aka aiko musu, in yaso duk mai korafi ya bari sai bayan an kammala bayyana sakamako a hadu a gaba.