Dan wasan kungiyar kwallon kafa ta Arsenal, Thomas Partey, ya Musulunta, adaidai daidai lokacin da kasar sa ta Ghana za ta kara da Najeriya wasan cancantar zuwa gasar cin kofin duniya wanda za a yi a kasar Qatar na shekarar 2022.
Wani dan jaridar wasanni da ke zaune a Birtaniya Connor Humm, ya rawaito a ranar Juma’a cewa, musuluntar Partey da hoton dan wasan tsakiyar Ghana rike da Alkur’ani mai girma.
Dan wasan tsakiyar mai shekaru 28, ya koma Arsenal ta Ingila daga Atletico Madrid ta Spain a shekarar 2020.
Musuluntar Thomas Partey ya zo