Tsohon gwamnan jihar Anambra, Peter Obi ya fice daga jam’iyyar adawa ta PDP.
Obi ya sanar da murabus din nasa ne a wata takarda mai dauke da kwanan wata 20, wacce ya aike wa shugaban jam’iyyar na kasa.
Ficewar sa daga jam’iyyar na iya nasaba da cewa damarsa na lashe zaben fidda gwani na jam’iyyar ta yi kadan.
A wata wasika da ya aike wa shugaban jam’iyyar sa ta PDP Agulu Ward II, dan takarar shugaban kasa a 2023 ya sanar da shi ficewar sa daga babbar jam’iyyar adawa a hukumance.
Har yanzu dai ba a bayyana ko Obi zai tsaya takarar Shugaban kasa a karkashin wata jam’iyya ba.