Dan majalisar dokokin jihar Katsina mai wakiltar mazabar Bakori, Hon. Ibrahim Kurami, ya rasu a birnin Madina na kasar Saudiyya.
Abokin hamayyar siyasar Kurami, Alhaji Nasiru Danguga ne ya bayyana hakan a cewar rahotanni.
Ya ce dan majalisar ya rasu ne a kasar Saudiyya a lokacin da yake gudanar da aikin Umara.
A cewarsa, hukumomin Saudiyya za su gudanar da Sallar jana’izarsa da kuma binne shi.