Alhaji Shamsudeen Dambazau, dan majalisar tarayya mai wakiltar mazabar Takai/ Sumaila a jihar Kano ya bayyana matakinsa na ficewa daga jam’iyyar All Progressives Congress (APC).
A wata sanarwa da ya fitar a ranar Litinin, Dambazau ya bayyana cewa, ya fice daga jam’iyyar APC zuwa jam’iyyar New Nigeria People’s Party (NNPP) karkashin jagorancin Dr Rabi’u Kwankwaso.
A cewar sa, ci gaban da bai dace ba a jam’iyya mai mulki ta APC a jihar ya sa ya dauki matakin da ya dace.
Ya jaddada cewa dole ne a yi sadaukarwa ta gaskiya a wani yunkuri na magance “matsalolin kasa da al’umma” don haka akwai bukatar a ci gaba.