Ɗaliban jami’o’i a jihar Kano, sun fito zanga-zanga, domin nuna rashin jnn daɗinsu kan yajin aikin da ƙungiyar Malaman Jami’o’i ta ASUU ke yi a fadin kasar nan.
Sun fara tattakin ne daga karkashin gadar kofar Nasarawa, sannan suka shiga gidan Murtala domin isar da sakonsu ga Kwamishinayar da ke kula da manyan makarantu.
An samar da jami’an tsaro na DSS da ƴan sanda daga ƙofar Nasarawa zuwa dukkan mahaɗa ta zuwa gidan gwamnatin Kano, da karkashin gadar Nasarawa. In ji BBC.
Tun a makon jiya ƙungiyar ɗaliban ta ƙasa NANS ta ce, za ta ƙaddamar da zanga-zanga a manyan biranen Najeriya kan yajin aikin ASUU.