An yi waje da tawagar Najeriya ta Flamingos daga gasar cin kofin duniya ta mata ‘yan kasa da shekaru 17 da ke wakana a kasar Indiya.
Najeriya ta fafata ne da kasar Colombia a yau Laraba bayan sun tashi canjaras.
Wasan ya kai ga bugun daga kai sai mai tsaron raga da ci 6 da 5.
Colombia na jiran kasar Jamus ko Spain a wasan karshe da za a fafata a ranar Lahadi.