Shugaban kasa Muhammadu Buhari zai bar Najeriya a yau Talata zuwa kasar Belgium, domin halartar wani taron shugabannin duniya.
Sanarwar da mai taimakawa Buhari a harkokin yada labarai, Shehu Garba, ta ce, shugaban zai dawo Najeriya ranar Asabar mai zuwa.
Sanarwar ta karanta cewa, Muhammadu Buhari zai bar Abuja, domin halartar taron shugabannin kasashen Turai da na Afirka da kuma shugabannin kungiyoyi da dama a taron kungiyar Tarayyar Turai da kasashen Afirka (EU da AU) karo na 6 a birnin Brussels na kasar Belgium.
Kuma a na sa ran shugaban kasa Muhammadu Buhari, zai dawo kasar nan a ranar Asabar.