Shugaban kasa, Muhammadu Buhari, ya bar Abuja domin zuwa duba lafiyarsa a kasar Ingila.
A cewar fadar shugaban kasar, a na sa ran Buhari zai shafe makonni biyu a Landan.
Shugaban ya bar Abuja zuwa kasar Ingila ranar Lahadi.
Tun a cikin tsakiyar makon nan ne shugaba Muhammadu Buhari, ya fasa zuwa kasar Ingila, sabanin cewa a baya zai wuce daga kasar Kenya kai tsaye, sai dai sanarwar ta sauya cewa, sai ya dawo gida Najeriya sannan ya wuce birnin Landan.