Shugaban kasa Muhammadu Buhari, ya rantsar da sabbin kwamishinonin hukumar kula da yawan al’umma ta kasa (NPC) da kuma hukumar yaki da cin hanci da rashawa da sauran laifuka (ICPC).
Rantsarwar ya kasance gabanin taron majalisar zartarwa ta tarayya na yau, wanda kuma shugaba Buhari ke jagoranta a fadar shugaban kasa dake Abuja.
Kwamishinonin NPC sun hada da: Cif Benedict Ukpong Effiong (Akwa Ibom), Misis Gloria Fateya Izonfo (Bayelsa), Kupchi Patricia Ori Iyanya (Benue), Dr Haliru Bala (Kebbi), da Dr Eyitayo Oyekunle Oyetunji (Oyo).
Kwamishinonin ICPC da aka rantsar sun hada da Mataimakin Sufeto Janar na ‘yan sanda, AIG, Olugbenga Adeyanju, rtd (Jihar Ekiti), Sanata Anthony Agbo (Ebonyi), Anne Otelafu Odey (Cross River), Alh. Goni Ali Gujba (Yobe), da Dr Louis Solomon Mandama (Adamawa).
Majalisar dattawa ta tabbatar da su dukan su tun a watan jiya.
A halin da ake ciki, shugaban kasar yana jagorantar taron majalisar zartarwa na mako-mako a zauren majalisar da ke fadar shugaban kasa.