Shugaban kasa Muhammadu Buhari ya rantsar da mai shari’a Olukayode Ariwoola a matsayin babban jojin Najeriya, CJN.
An rantsar da Ariwoola a ranar Litinin a zauren majalisar da ke Abuja.
Ya karbi mulki daga hannun tsohon CJN, Ibrahim Tanko Muhammad wanda ya yi murabus a ranar Litinin, saboda rashin lafiya.
An haifi Mai shari’a Ariwoola ne a ranar 22 ga watan Agustan shekarar 1958, kuma a halin yanzu shi ne babban alkalin kotun koli.
Tsohon Alkalin Kotun Daukaka Kara ne kuma an daukaka shi zuwa Kotun Koli, bayan sauya shekarsa daga Babbar Kotun Jihar Oyo.
Ariwoola ya fara karatunsa ne a garinsu Iseyin a makarantar Muzahara ta karamar hukumar Oluwole a karamar hukumar Iseyin ta jihar Oyo tsakanin 1959 zuwa 1967.