Shugaban kasa Muhammadu Buhari ya amince da nadin Mista Leke Pitan a matsayin Manajan Daraktan Bankin Masana’antu na tsawon shekaru biyar.
A wata sanarwa da mataimaki na musamman kan harkokin yada labarai ya fitar a ranar Talatar, Ministan Masana’antu, Kasuwanci da Zuba Jari, Ifedayo Sayo, ta ce, sabon nadin wanda zai fara aiki daga ranar 27 ga watan Mayun 2022, an mika shi ne ta wata wasika mai dauke da sa hannun sakataren gwamnati na tarayya, Boss Mustapha da kwanan wata 11 ga Maris, 2022.
Haka kuma, shugaban ya amince da nadin Alhaji Dikko Aliyu Abdulrahaman a matsayin shugaban bankin na wucin gadi na tsawon shekaru biyar daga ranar 27 ga Mayu, 2022.