Shugaban kasa Muhammadu Buhari ya rubutawa majalisar dokoki wasika yana neman a tabbatar da sunayen ministoci 7, domin maye gurbin wadanda suka yi murabus domin cimma burinsu na takarar shugaban kasa da na gwamna.
Daga cikin Ministoci da aka amince da nadin a Majalisar Buhari sun hada da, Henry Iko, Jihar Abia, Umana Umana, Akwa Ibom, Ekuma Joseph, Jihar Ebonyi, Goodluck Opiah, Jihar Imo, Umar El-Yakub, Jihar Kano, Ademola Adegoroye, Jihar Ondo. da Odum Odi, Jihar Riba.
Ku tuna cewa an samu baraka a tsakanin mambobin majalisar zartarwa ta tarayya bayan ficewar Emeka Nwajiuba, karamin ministan ilimi, Rotimi Amaechi, ministan sufuri, da Ogbonnaya Onu, ministan kimiyya da fasaha da dai sauransu.