fidelitybank

Da Dumi-Dumi: Buhari ya amince da dala miliyan 8.5 a fara kwaso ‘yan Najeriya daga Ukraine

Date:

Shugaban kasa, Muhammadu Buhari, ya amince da bayar da dala miliyan 8.5 ga ma’aikatun harkokin kasashen waje da ayyukan jin kai, magance bala’o’i, da ci gaban jama’a, domin kwashe ‘yan Najeriya sama da 5,000 (masu rijista da marasa rijista) da ke makale a kasar Ukraine.

Karamin Ministan Harkokin Waje, Zubairu Dada ne ya bayyana hakan a ranar Laraba.

Ministan ya shaidawa manema labarai na fadar gwamnati, bayan taron majalisar zartarwa ta tarayya cewa, za a aike da jiragen sama guda uku zuwa kasashe hudu.

A cewarsa, kasashen da za a fara jigilar jiragen sun hada da Poland, Hungary, Slovakia, da Romania.

Ana sa ran jiragen biyu daga Air Peace da kuma na Max Air za su gudanar da aikin kwashe mutanen.

Dada ya ce, dukkan hukumomin sun ba da cikakken kayan aiki, domin tabbatar da cewa jiragen sun tashi a ranar Laraba domin fara kwashe su. Sun yi nuni da cewa, jiragen za su yi tafiya da yawa har sai an kammala aiki.

leadership news

Subscribe to Our VIP Newsletter

[newsletter_signup_form id=1]

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here

Share post:

Popular

More like this
Related

Gwamnatin Tinubu ta kama-karya ce – Atiku

Tsohon mataimakin shugaban kasa, Atiku Abubakar ya ce, hare-haren...

An gayyaci El-Rufa’i ka n zargin tayar da rikici a Kaduna

Rundunar ƴansandan jihar Kaduna, sun buƙaci tsohon gwamnan jihar...

Badakalar Naira biliyan 1.17 ta sake kunno kai a gwamnatin Kano

Rikicin rashawa da ya dabaibaye gwamnatin jihar Kano ya...

Ba za mu daga kafa ga duk wanda ya takale mu ba – China

Shugaba Xi Jinping na China, ya ce babu wani...

Nigeria Air ba na bogi ba ne – Hadi Sirika

Tsohon Ministan sufurin jiragen sama na Najeriya, Hadi Sirika,...

Amurka ta mika wa Najeriya tallafin abinci miliyan 32.5

Gwamnatin Amurka ta bayar da tallafin dala miliyan 32.5...

Gwamnatin Kano ta gargadi kungiyar ACF

Gwamnatin jihar Kano ta gargaɗi ƙungiyar Arewa Consultative Forum...

Operation Kukan Kura ya yi aiki sosai a Kano – CP Bakori

Hukumar ‘Yan Sanda ta Jihar Kano ta kaddamar da...

An sanya dokar ta bace a Makabartun Kano

Shugaban ƙaramar hukumar Nassarawa a Kano Honarabul. Yusuf Shuaibu...

An ga ‘Yar shekara 13 Fatima a rataye a Kano

Iyaye da sauran ‘yan uwa na cikin juyayi kan...

‘Yansanda sun kama Linga da Guchi rikakkun ‘yan Daba a Kano

Rundunar ’yan sandan jihar Kano ta kama Mohammed Isma’il...

Tinubu ya sauka da kwari bayan ya dawo daga Brazil

Shugaba Bola Ahmed Tinubu ya koma Najeriya bayan kammala...
X whatsapp