Akalla masu sana’ar tattara karafa wato ‘yan gwangwan 55 ne suka rasa rayukansu a wasu hare-hare da mayakan Boko Haram suka hada kai a cikin makonni uku da suka gabata a Borno.
Kwamishinan ‘yan sandan jihar, Abdu Umar ne ya bayyana haka yayin da yake magana a gefen taron masu ruwa da tsaki na tsaro a ranar Asabar a Maiduguri.
Masu ruwa da tsakin sun hada da ‘yan sanda, Sojoji, Tsaron Najeriya da Civil Defence (NSCDC), da kuma DSS da dai sauransu.
Taron dai an yi shi ne domin tattaunawa tare da samar da mafita kan hare-haren da ake kaiwa masu tarin karafa a jihar.
Umar ya ce, ‘yan ta’addan sun kashe masu tarin karafa 32 a kauyen Modu da ke karamar hukumar Kala-Balge yayin da wasu 23 suka kashe a kauyen Mukdala na karamar hukumar Dikwa.
Ya ce wadanda lamarin ya rutsa da su sun kutsa cikin dazuzzukan da ke da tazarar kilomita 25 daga garuruwan ba tare da sanar da jami’an tsaro tattara karafa ba.
Ya ce, Gwamna Babagana Zulum ya umurci hukumomin tsaro da su dauki matakan dakile kashe-kashen, domin dakile afkuwar lamarin nan gaba.