fidelitybank

Da Dumi-Dumi: Boko Haram sun kai hari Chibok

Date:

‘Yan ta’addan Boko Haram da ke samun goyon bayan kungiyar Da’ish, Lardin Islamic State West Africa da ake kira Jamā’at Ahl as-Sunnah lid-Da’wah wa’l-Jihād, suna kai farmaki a kauyen Kautikari da ke karamar hukumar Chibok a Jihar Borno.

SaharaReporters ta tattaro cewa, ‘yan ta’addan sun mamaye garin ne a ranar Talata, inda suka rika harbe-harbe a kai a kai yayin da mazauna unguwar suka tsere zuwa cikin dajin domin tsira da rayukansu.

Sojojin da aka ajiye a sansanin sojojin gaba (FOB) da ke Kada mai tazarar kilomita 2 daga Kautukari, suma maharan sun tarwatsa su.

“An kai wa al’umma hari, wannan shi ne hari na hudu a bana kadai, don Allah a yi mana addu’a,” kamar yadda wani mazaunin garin ya shaida wa SaharaReporters.

A watan Disamba 2021 da Janairu 2022, Kautikari ya fuskanci hare-hare daga masu tayar da kayar baya wadanda suka sace mata da yara da dama.

Har ila yau, maharan sun yi wa wata majami’a a yankin wuta a yayin hare-haren.

Hare-haren da aka kai a yankunan Chibok, musamman wanda ya faru a watan Janairun 2022, ya sanya gwamnan jihar Borno, Farfesa Babagana Umara Zulum, ya ziyarci yankin domin karfafa gwiwar jama’a da kuma jami’an tsaro da aka jibge a karamar hukumar.

A yayin ziyarar gwamnan ya gana da iyalan mata 22 da maza biyu da maharan suka yi garkuwa da su inda ya bukaci su ci gaba da dogara ga Allah ta hanyar addu’a.

nigerian 
news today

Subscribe to Our VIP Newsletter

[newsletter_signup_form id=1]

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here

Share post:

Popular

More like this
Related

Gwamnatin Tinubu ta kama-karya ce – Atiku

Tsohon mataimakin shugaban kasa, Atiku Abubakar ya ce, hare-haren...

An gayyaci El-Rufa’i ka n zargin tayar da rikici a Kaduna

Rundunar ƴansandan jihar Kaduna, sun buƙaci tsohon gwamnan jihar...

Badakalar Naira biliyan 1.17 ta sake kunno kai a gwamnatin Kano

Rikicin rashawa da ya dabaibaye gwamnatin jihar Kano ya...

Ba za mu daga kafa ga duk wanda ya takale mu ba – China

Shugaba Xi Jinping na China, ya ce babu wani...

Nigeria Air ba na bogi ba ne – Hadi Sirika

Tsohon Ministan sufurin jiragen sama na Najeriya, Hadi Sirika,...

Amurka ta mika wa Najeriya tallafin abinci miliyan 32.5

Gwamnatin Amurka ta bayar da tallafin dala miliyan 32.5...

Gwamnatin Kano ta gargadi kungiyar ACF

Gwamnatin jihar Kano ta gargaɗi ƙungiyar Arewa Consultative Forum...

Operation Kukan Kura ya yi aiki sosai a Kano – CP Bakori

Hukumar ‘Yan Sanda ta Jihar Kano ta kaddamar da...

An sanya dokar ta bace a Makabartun Kano

Shugaban ƙaramar hukumar Nassarawa a Kano Honarabul. Yusuf Shuaibu...

An ga ‘Yar shekara 13 Fatima a rataye a Kano

Iyaye da sauran ‘yan uwa na cikin juyayi kan...

‘Yansanda sun kama Linga da Guchi rikakkun ‘yan Daba a Kano

Rundunar ’yan sandan jihar Kano ta kama Mohammed Isma’il...

Tinubu ya sauka da kwari bayan ya dawo daga Brazil

Shugaba Bola Ahmed Tinubu ya koma Najeriya bayan kammala...
X whatsapp