Bam ya hallaka wani ministan yanki da ɗansa a wani hari da aka kai kudu maso yammacin kasar Somaliya.
An kai harin ne na birnin Baidoa kan Hassan Ibrahim Lugbur, ministan shari’a na yankin kudu maso yammacin ƙasar – a lokacin da yake barin masallaci bayan Sallar Juma’a.
Mutane da dama da suka haɗa da masu tsaronsa sun jikkata.
A farkon wannan makon ne aka kashe magajin garin birnin Merka da ke gaɓar teku – a dai wannan yankin na Somaliya.
Ƙungiyar masu ikirarin jihadi ta Al Shabab ta ce ita ta kai harin. In ji BBC.